31 Oktoba 2020 - 09:20
Iraki:Sojojin Kasar Sun Rusa Rumbunan Ajiyar Makamai Na Daesh A Kirkuk

Wata majiyar sojojin kasar Iraki ta bayyana cewa, sojojin kasar sun sami nasarar rusa rumbunan ajiyar makamai na kungiyar Daesh a Lardin Kirkuk a jiya jumma’a.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labarabn ‘Bagadadul- Yaum’ ya nakalto majiyar ta na cewa wurare hudu ne a karkashin kasa, wadanda mayakan na Deash suke amfani da su don boye makamai a garin “Daquq” wadanda sojojin suka rusa a jiya jumma’a.

Labarin ya kara da cewa akwai rumbunan ajiye makamai da kuma abubuwan fashewa a wadannan mabuya ta karakshin kasa mallakin kungiyar.

Har’ila yau labarin ya nakalto kwamandan dakaru “masana ilmin kimiyyar lissafi” yana cewa shi ya jagoranci rundunar wajen wargaza makaman.

Tun shekara ta 2017 ne dai dakarun Hashdushaabi da sojojin kasar ta Iraki su ka kawo karshen mamayar da kungiyar ta Daesha tayiwa arewacin kasar, amma har yanzun akwai ragowarsu wadanda suke kokarin kai hare-hare nan da can a cikin kasar.

342/